Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGanduje: Tikitin Obi da Kwankwaso ba zai yi nasara a Kano ba...

Ganduje: Tikitin Obi da Kwankwaso ba zai yi nasara a Kano ba a 2027

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a ƙarƙashin jam’iyyar NDC ba zai yi nasara a Jihar Kano ba a babban zaɓen shekarar 2027.

Siyasarmu TV ta rawaito cewa Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata.

A cewarsa, haɗakar Obi da Kwankwaso ba ta da isasshen ƙarfin siyasa ko tarihin mulki da zai sa ta samu goyon bayan al’ummar Jihar Kano.

Ganduje ya kuma jaddada cewa jam’iyyar APC na ci gaba da kasancewa mai ƙarfi a Kano, yana mai cewa ta gina tubali mai ƙarfi da zai ba ta damar ci gaba da samun goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da riƙe tasirinta a jihar duk da sauye-sauyen siyasa da haɗakar jam’iyyun adawa da ake gani gabanin zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments