Akalla mutum huɗu sun rasa rayukansu, wasu da dama sun jikkata, yayin da ɗaruruwan iyalai suka rasa matsugunansu sakamakon wata mummunar guguwar iska da ruwan sama mai ƙarfi da ta afku a ƙaramar hukumar Kware ta jihar Sokoto ranar Asabar. Bala’in ya kuma lalata gidaje da dama tare da yin ɓarna ga muhimman gine-ginen gwamnati, ciki har da makarantar firamare da asibiti.
Bayan aukuwar lamarin, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) reshen Sokoto ta kai ziyara yankunan da abin ya shafa domin tantance girman asarar da aka yi da kuma gano irin agajin gaggawar da waɗanda bala’in ya rutsa da su ke buƙata. Yankunan da aka ziyarta sun haɗa da Mallamawa, Mai Mushe, Kaura, Sabon Gari, Rungin Tsamiya da sauran ƙauyukan da ke kewaye.
Rahoton farko da NEMA ta fitar ya nuna cewa ɗaruruwan iyalai sun rasa muhallansu, inda gidaje da dama suka rushe gaba ɗaya ko kuma suka samu mummunar ɓarna. Haka kuma, mutane da dama sun samu raunuka daban-daban, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum huɗu.
Hukumar ta bayyana cewa manufar wannan tantancewar ita ce gano ainihin irin barnar da aka yi domin a hanzarta kai kayan tallafi da sauran agajin gaggawa ga al’ummomin da abin ya shafa. Ta ce za ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa waɗanda bala’in ya shafa sun samu taimakon da ya dace.
NEMA ta kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da tattara cikakken bayanai kan girman asarar da aka yi, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin rage wahalhalun da waɗanda abin ya shafa ke fuskanta. Hukumomin sun yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da haɗin kai yayin da ake ci gaba da ayyukan agaji da tantance cikakken tasirin wannan bala’i.