Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiICPC ta gurfanar da likitan El-Rufai kan zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na...

ICPC ta gurfanar da likitan El-Rufai kan zargin ƙirƙirar rahoton lafiya na bogi

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta gurfanar da Dr. Bello Abubakar, ƙwararren likitan cutar daji a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, bisa zargin ƙirƙira da amfani da rahoton lafiya na bogi.

A cewar ICPC, ana zargin likitan ya samar da rahoton ne domin tallafa wa buƙatar neman beli da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa hujjar rashin lafiya.

Hukumar ta ce zargin ya shafi amfani da takardun da ake zargin ba su dace ba a gaban hukuma, lamarin da ta ce ya sa aka gurfanar da wanda ake zargin domin amsa tuhume-tuhumen da ake masa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken martani daga Dr. Bello Abubakar ko kuma lauyoyin da ke kare shi kan zarge-zargen da ICPC ta gabatar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments