Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai halarci zama na 81 na Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda za a gudanar a birnin New York na Amurka a watan Satumba, inda zai gabatar da jawabi ga shugabannin ƙasashen duniya.
Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa zai halarci taron, tare da amincewa da dukkan shirye-shiryen da Najeriya ta yi domin wakiltar ƙasar a babban taron na bana.
Ana sa ran za a buɗe zama na 81 na Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 8 ga Satumba, yayin da shugabannin ƙasashe za su tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da sauyin yanayi, ci gaba mai ɗorewa, zaman lafiya da tsaro na ƙasa da ƙasa, da sauran manyan ƙalubalen da duniya ke fuskanta.
Halartar Shugaba Tinubu na daga cikin damar da Najeriya za ta samu wajen bayyana matsayinta kan batutuwan duniya da kuma ƙarfafa dangantakarta da sauran ƙasashe.