Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar Kano bisa abin da ya bayyana a matsayin jajircewarta wajen kare martaba da mutuncin Masarautar Kano.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron bita na kwanaki uku da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shirya a Kaduna, wanda ya haɗa hakimai da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya daga ƙananan hukumomin jihar.
A cewarsa, Masarautar Kano na ci gaba da yaba wa gwamnatin jihar kan irin goyon bayan da take bai wa harkokin masarautu, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen ƙarfafa martaba da kimar sarautun gargajiya.
Sarkin ya kuma yi kira ga hakimai da sauran masu riƙe da sarauta da su ci gaba da aiki cikin haɗin kai, adalci tare da bin doka wajen gudanar da ayyukansu domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.