An kama wasu ‘yan ƙasar Sin uku da wasu masu haƙar ma’adinai ‘yan Najeriya bisa zargin gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a ƙauyen Amba da ke ƙaramar hukumar Kokona a jihar Nasarawa.
An kama su ne bayan Mataimakin Gwamnan jihar, Emmanuel Agbadu Akabe, ya jagoranci wata babbar tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da ake zargin ana gudanar da haƙar ma’adinan ba tare da izini ba.
A yayin samamen, jami’an tsaro sun ƙwace wasu ma’adinai da ake zargin an haƙo waɗanda aka adana a cikin kwalaye, tare da wasu kayayyakin aiki da ake amfani da su wajen gudanar da haƙar ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba.
Daga cikin kayayyakin da aka ƙwace akwai na’urorin CCTV da sauran kayan aiki da ake zargin an girka domin sa ido da sauƙaƙa gudanar da ayyukan haƙar ma’adinan.
Da yake magana bayan samamen, Mataimakin Gwamna Akabe ya ce shi da kansa ya jagoranci aikin ne bayan samun rahotanni cewa har yanzu ana ci gaba da haƙar ma’adinai a yankin duk da umarnin gwamnati na dakatar da ayyukan. Ya ce abin takaici ne yadda aka yi watsi da umarnin dakatarwar.
Akabe ya kuma yi tambaya kan yadda baƙi daga ƙasashen waje da ba su da cikakkun takardun izini ke samun damar shiga Najeriya domin haƙar ma’adinai. Ya jaddada cewa gwamnatin Nasarawa ba za ta amince da duk wani kasuwanci da ya saɓa wa doka ba, kuma za ta tabbatar da bin doka da oda.
Ya bayyana cewa duk da yake harkar haƙar ma’adinai tana ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar za ta ci gaba da kare muradun al’ummomin da abin ya shafa tare da tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa babu wata yarjejeniya da aka yi da al’ummar yankin kan nauyin da kamfanin zai ɗauka ga al’umma ko kuma tantance tasirin muhalli kafin fara aikin.
Mataimakin gwamnan ya gargaɗi cewa duk wanda bincike ya kama da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada. Ya kuma ce za a ci gaba da rufe wuraren haƙar ma’adinan har sai an kammala shari’o’in da suka shafi yankin.
Ta bakin mai fassara, ‘yan ƙasar Sin da aka kama sun ce sun fara aikin haƙar ma’adinai a yankin tun bara, kuma suna yin aikin ne a madadin wasu shugabanninsu da ke zaune a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a gurfanar da shi a gaban kotu.