Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMasu rajin kare haƙƙin dan adam sun bukaci a yi adalci kan...

Masu rajin kare haƙƙin dan adam sun bukaci a yi adalci kan mutuwar Mary Habila

Ana ci gaba da samun kiraye-kirayen a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar Mary Habila, mai shekaru 26, wadda aka tsinci gawarta a gidan Ministan Ayyuka na Tarayya, David Umahi, da ke Jihar Ebonyi.

Ana ci gaba da samun kiraye-kirayen a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar Mary Habila, mai shekaru 26, wadda aka tsinci gawarta a gidan Ministan Ayyuka na Tarayya, David Umahi, da ke Jihar Ebonyi.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, ƙungiyoyin farar hula da wasu ’yan siyasa sun buƙaci hukumomi su gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano ainihin musabbabin mutuwar, tare da tabbatar da adalci da gaskiya ga iyalan marigayiyar.

A nasa ɓangaren, David Umahi ya musanta duk wata alaƙa da ake danganta shi da mutuwar Mary Habila. Ya ce marigayiyar ta kasance tamkar ’yarsa, kuma shi ne ya nemi a gudanar da gwajin gawa domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi ta bayyana cewa iyalan marigayiyar ba su amince da a yi gwajin gawa ba. Ta kuma tabbatar da cewa bincike kan lamarin na ci gaba domin gano hakikanin abin da ya jawo mutuwar.

Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwar Mary Habila ba, yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon binciken hukumomi. Masu ruwa da tsaki na ci gaba da kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaskiya, adalci da kuma bayyana sakamakonsa domin kawar da duk wata shakka da ke tattare da lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments