Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiFiye da mutum 1,000 sun tsere daga gidajensu bayan harin ’yan bindiga...

Fiye da mutum 1,000 sun tsere daga gidajensu bayan harin ’yan bindiga a Benue

Fiye da mutane 1,000 sun bar gidajensu sakamakon wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai kan al’ummar Ankpechi da ke gundumar Oglewu a Ƙaramar Hukumar Ohimini, jihar Benue.

Rahotanni sun ce maharan sun mamaye yankin da sanyin safiyar Alhamis, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin guduwa zuwa ƙauyuka da al’ummomin da ke makwabtaka domin tsira da rayukansu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da kuma hana sake kai irin wannan hari.

Harin ya biyo bayan wasu hare-hare da aka kai a yankunan da ke kusa, abin da ke nuna ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro a jihar Benue.

Hare-haren sun janyo asarar matsugunai, sun tarwatsa rayuwar al’umma, tare da kawo cikas ga ayyukan noma a jihar da ake kallon a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin samar da abinci a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments