Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo ta kama wani mutum mai suna Amos Paul bisa zargin kona al’aurar ’yarsa mai shekaru 10 da ƙarfen guga mai zafi a matsayin hukunci saboda tana yin fitsari kwance.
Lamarin ya faru ne a yankin Unaun, Upenme da ke ƙaramar hukumar Owo, inda aka kai rahotonsa ga ‘yan sanda a ranar Alhamis. Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin tare da cafke wanda ake zargin.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ya ce yarinyar ta samu munanan raunuka sakamakon ƙonawar, kuma an garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya na jihar, inda ake ci gaba da ba ta kulawa.
Ya ƙara da cewa an miƙa shari’ar zuwa sashen kula da mata da yara na rundunar domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ondo, CP Felix Ohagwu, ya yi Allah wadai da abin da ya faru, yana mai bayyana lamarin a matsayin zalunci da rashin mutunta ɗan’adam. Ya tabbatar da cewa rundunar za ta tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da hannu a cin zarafin yara ko wasu marasa ƙarfi, tare da kira ga jama’a da su rika kai rahoton irin waɗannan laifuka ga hukumomin tsaro cikin gaggawa.