Tawagar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta kai wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026 bayan ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe mai cike da ɗaukar hankali.
Bayan tashi daga wasan, wasu daga cikin ‘yan wasan Argentina sun ɗaga wani babban kyalle mai ɗauke da rubutun “Las Malvinas son Argentinas” ma’ana “Tsibirin Falkland mallakin Argentina ne.” Daga cikin waɗanda aka gani da allon akwai Lisandro Martínez, Giovani Lo Celso, Cristian Romero da kuma kyaftin Lionel Messi.
Wannan mataki ya sake tayar da muhawara kan rikicin mallakar Tsibirin Falkland (Las Malvinas), wanda ya janyo yaƙi tsakanin Birtaniya da Argentina a shekarar 1982. A wannan yaƙi, mutane 907 ne suka mutu, ciki har da sojojin Birtaniya 255, bayan da Birtaniya ta sake ƙwace tsibiran daga hannun Argentina.
Tun kafin wasan, FIFA ta haramta shigar da tutoci ko allunan da ke ɗauke da saƙonnin siyasa game da Falkland a filin wasa. Saboda haka, ana sa ran hukumomin ƙwallon ƙafa za su binciki matakin da ’yan wasan Argentina suka ɗauka bayan wasan.
Rikicin ya ƙara ɗaukar hankali ne bayan Ministan Harkokin Wajen Argentina, Pablo Quirno, ya sake jaddada cewa tsibiran na ƙasarsu ne, yayin da gwamnatin Birtaniya ta nace cewa kuri’ar raba gardama da aka gudanar a shekarar 2013, wadda kashi 99.8 cikin 100 na mazauna tsibirin suka zaɓi ci gaba da kasancewa ƙarƙashin Birtaniya, ta tabbatar da matsayin tsibiran.
A filin wasa kuwa, Ingila ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Antony Gordon a farkon wasan. Sai dai Enzo Fernández ya farke wa Argentina saura mintuna kaɗan a tashi daga wasa, kafin Lautaro Martínez ya zura ƙwallon nasara a cikin lokacin ƙarin da aka ba da, lamarin da ya tabbatar da nasarar Argentina da kuma tikitin zuwa wasan ƙarshe inda za ta kara da Spain.