Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAdo Doguwa: Buhari ya jagoranci Najeriya bisa adalci da riƙon amana

Ado Doguwa: Buhari ya jagoranci Najeriya bisa adalci da riƙon amana

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gudanar da mulki bisa gaskiya, adalci da riƙon amana, yana mai cewa salon jagorancinsa ya yi daidai da ƙa’idojin shugabanci da addinin Musulunci ya tanada.

Doguwa ya bayyana hakan ne yayin taron tunawa da cika shekara guda da rasuwar Buhari da aka gudanar a Abuja.

Ya ce Najeriya ta yi babban rashi sakamakon mutuwar tsohon shugaban ƙasar, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke fuskantar ƙalubale daban-daban.

A cewarsa, Buhari bai yi amfani da mulki wajen tara wa kansa dukiya ba, kuma ya rayu wajen ba da fifiko ga hidimtawa ƙasa.

Ya kuma yaba da irin tarbiyyar da marigayin ya bai wa iyalansa.

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya da kishin ƙasa irin Buhari, waɗanda za su taimaka wajen shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka yi addu’o’i tare da tuna irin gudunmawar da marigayi Muhammadu Buhari ya bayar a lokacin da yake jagorantar Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments