Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYau shekara daya da rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yau shekara daya da rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu a ranar 13 ga Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan na ƙasar Birtaniya, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Bayan sanar da rasuwarsa, an kawo gawarsa gida Najeriya, inda aka gudanar da jana’izarsa a ranar 15 ga Yuli a garinsu na Daura da ke jihar Katsina, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Jana’izar ta samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da manyan jami’an gwamnati na daga cikin waɗanda suka halarci bikin bankwana da tsohon shugaban ƙasar.

Muhammadu Buhari ya jagoranci Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda ya kammala wa’adin mulki biyu a matsayin shugaban ƙasa.

Ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, inda ya bar mata da ‘ya’ya da sauran ’yan uwa.

Har yanzu ana ci gaba da tunawa da rayuwarsa da gudunmawar da ya bayar a harkokin siyasa da mulkin Najeriya.

Da me za ku iya tunawa da marigaya tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari?

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments