Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya yi zargin cewa wasu mambobin Majalisar Tarayya sun buƙaci ya ba su Naira miliyan 200 a matsayin cin hanci lokacin da ya je kare kasafin kuɗin ma’aikatar a farkon mulkinsa ƙarƙashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Dalung ya ce bayan gabatar da kasafin kuɗin ma’aikatar, an buƙace shi ya samar da kuɗin, amma ya shaida musu cewa babu wani tanadi a kasafin kuɗi da aka ware domin cin hanci, don haka bai san inda zai samo kuɗin ba.
Ya ce bayan amsar da ya bayar, an sallame shi daga taron, inda aka ce za a ci gaba da tattaunawa da Babban Sakataren Ma’aikatar.
Dalung ya kuma yi zargin cewa daga baya an rage rawar da yake takawa wajen kare kasafin kuɗi, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta zama ruwan dare a wasu ma’aikatun gwamnati, kuma hakan na raunana tsarin sa ido da gaskiya a harkokin gwamnati.
Sai dai zuwa lokacin wallafa rahoton, Majalisar Tarayya ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen da Dalung ya yi ba.