Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiFadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Peter Obi na barazanar hallaka shi

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin Peter Obi na barazanar hallaka shi

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, cewa gwamnatin tarayya na bibiyarsa tare da yi masa barazanar kashe shi.

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, cewa gwamnatin tarayya na bibiyarsa tare da yi masa barazanar kashe shi.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da Chude Jideonwo, inda ya ce ba shi da tabbacin zai kai ga zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai zargin gwamnatin tarayya da hana shi gudanar da harkokinsa da kuma takura masa.

Sai dai Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa ba su da hujja kuma an yi su ne domin jawo tausayi da yaɗa farfaganda.

Onanuga ya kuma ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta da wata niyya ta tsananta wa Obi ko kuma Bankin Fidelity, wanda ake cewa yana da hannun jari a ciki.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da inganta rayuwar ’yan Najeriya, ba shiga rikice-rikicen siyasa ko takura wa ’yan adawa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments