Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa za ta gudanar da zama na musamman da masu ruwa da tsaki daga yankunan Ɗorayi da Kewaye domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke addabar al’ummomin yankunan.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan lokacin da gamayyar kwamitocin tsaro na Ɗorayi da Kewaye suka kai masa ziyara a yau domin tattaunawa kan hanyoyin ƙarfafa tsaro da samar da zaman lafiya.
Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya himmatu wajen ɗaukar duk matakan da suka dace domin daƙile matsalolin tsaro da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunan.
CSP Kiyawa ya yabawa shugabannin kwamitocin tsaron bisa irin gudummawar da suke bayarwa ga hukumomin tsaro, yana mai bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro.
Ziyarar ta samu halartar shugabannin gamayyar kwamitocin tsaro na Ɗorayi da Kewaye ƙarƙashin jagorancin Malam Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo, inda bangarorin biyu suka jaddada aniyar ci gaba da haɗa kai domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.