Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya amince da naɗin Ahmed Tijjani Musa Jega a matsayin Mai Ba Shi Shawara na Musamman kan harkokin makabartu a jihar.
Sanarwar naɗin ta fito ne ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu B. Tafida, inda ya bayyana cewa naɗin ya fara aiki nan take.
A cewar sanarwar, sabon mai ba da shawarar zai rika bai wa gwamnatin jihar shawarwari kan yadda za a inganta gudanarwa, tsari da kula da makabartu a faɗin Jihar.
Naɗin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka na cike muƙamai da nufin inganta ayyukan gwamnati da samar da ingantaccen tsarin gudanarwa a fannoni daban-daban.
Ana sa ran Ahmed Tijjani Musa Jega zai yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da kyakkyawan tsari da gudanar da harkokin makabartu yadda ya kamata.