Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi gargadin cewa wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa yaƙin basasar Najeriya na shekarar 1967 har yanzu suna nan, yana mai jaddada cewa dole ne a ɗauki matakan da suka dace domin hana sake afkuwar irin wannan rikici.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake karɓar kundin bincike, takardu, bidiyo da shaidun gani da ido kan kisan gillar Asaba, wanda Shugaban Asaba Memorial Trust, Chuck Nduka-Eze, ya tattara, a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta.
Ya ce sake fuskantar yaƙin basasa abu ne da bai kamata a yi tunaninsa ba, yana mai cewa Najeriya ta riga ta biya babban farashi sakamakon yaƙin basasar da ta taɓa fuskanta, don haka wajibi ne a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.