Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun cafke tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Uche Nnaji, a Filin Jirgin Sama na Akanu Ibiam International Airport da ke jihar Enugu.
Rahotanni sun ce an kama Nnaji ne da sanyin safiyar Laraba yayin da yake ƙoƙarin hawa wani jirgin sama mai zaman kansa da zai nufi Abuja.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama tsohon ministan ne bisa buƙatar Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa, wadda ke gudanar da bincike a kansa kan wasu zarge-zarge.