Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroAn ƙone mutane 18 da ransu a rikicin jihar Neja

An ƙone mutane 18 da ransu a rikicin jihar Neja

Aƙalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu a jihar Neja sakamakon sabon rikici da ya ɓarke tsakanin al’ummomi a ƙaramar hukumar Rafi, kamar yadda rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Godoro da ke yankin Katako a daren Litinin, inda suka kashe wani matashi mai shekara 25.

A cewarsa, bayan wannan harin ne wasu mambobin ƙungiyar sa-kai suka tare hanya tare da kashe wani mutum mai shekara 28.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments