Aƙalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu a jihar Neja sakamakon sabon rikici da ya ɓarke tsakanin al’ummomi a ƙaramar hukumar Rafi, kamar yadda rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa lamarin ya samo asali ne bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Godoro da ke yankin Katako a daren Litinin, inda suka kashe wani matashi mai shekara 25.
A cewarsa, bayan wannan harin ne wasu mambobin ƙungiyar sa-kai suka tare hanya tare da kashe wani mutum mai shekara 28.