Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya jajanta wa gwamnatin jihar Legas da al’ummar jihar baki ɗaya kan ambaliyar ruwa da ta afku a jihar, wadda ta haddasa asarar dukiyoyi tare da jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali.
Atiku ya bayyana alhininsa kan wannan ibtila’i, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Ya kuma buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gaggauta kai agaji ga waɗanda suka rasa muhallansu da dukiyoyinsu.
Haka kuma, ya yi kira ga ’yan Najeriya da ƙungiyoyin agaji da su haɗa kai wajen tallafa wa waɗanda ambaliyar ta rutsa da su domin rage musu raɗaɗin halin da suke ciki.