Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da gina cibiyoyin tsaro da za su haɗa jami’an hukumomin tsaro daban-daban tare da girke kyamarorin tsaro na CCTV a sabbin gadar sama na Dan’Agundi da Tal’udu domin ƙarfafa tsaro a birnin Kano.
Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na jihar, Injiniya Marwan Ahmed Aminu, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Litinin.
Ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na haɗa ci gaban gine-ginen more rayuwa da inganta tsaro.
A cewarsa, za a fara gina cibiyoyin tsaron ne bayan kammala ayyukan gadar saman Dan’Agundi da Tal’udu, domin kare gine-ginen da kuma tabbatar da tsaron masu amfani da hanyoyin.
Ya bayyana cewa cibiyoyin za su ƙunshi jami’an:
Rundunar ’Yan Sanda
Hukumar NSCDC
Hukumar KAROTA Hukumar Hisbah
Ƙungiyoyin sa-kai (Vigilante)
Hukumar NDLEA
Sauran sun hada da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.
Kwamishinan ya kuma ce za a girke kyamarorin CCTV a gadar saman Dan’Agundi domin sa ido kan abubuwan da ke faruwa a wurin na tsawon sa’o’i 24 a rana.
A cewarsa, tsarin sa idon zai taimaka wa jami’an tsaro wajen bibiyar motsin jama’a, hana aikata laifuka, saurin kai ɗauki a lokutan gaggawa, da kuma ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano da masu amfani da hanyoyin.