Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeGhana na shirin gina sabon birni domin rage cunkoso an Accra

Ghana na shirin gina sabon birni domin rage cunkoso an Accra

Shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin gina sabon birni a wajen Accra tare da mayar da wasu manyan cibiyoyin gwamnati zuwa can domin rage cunkoson jama’a a babban birnin ƙasar.

Shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin gina sabon birni a wajen Accra tare da mayar da wasu manyan cibiyoyin gwamnati zuwa can domin rage cunkoson jama’a a babban birnin ƙasar.

Mahama ya bayyana hakan ne bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Accra, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata gidaje, hanyoyi da wuraren kasuwanci.

Ya ce duk da cewa gwamnati za ta ci gaba da inganta magudanan ruwa domin rage ambaliyar, akwai buƙatar ɗaukar mataki na dogon lokaci ta hanyar rage cunkoso a Accra.

A cewarsa, sabon birnin zai kasance da gidaje, cibiyoyin kasuwanci da ofisoshin gwamnati, tare da samar da hanyoyi, wutar lantarki da ruwan sha domin jawo hankalin jama’a da kamfanoni su koma yankin.

Shugaban ya ƙara da cewa ana sa ran aikin gina sabon birnin zai ɗauki kusan shekaru 20 kafin a kammala shi, yana mai bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin birane da rage matsin lamba da ake fuskanta a Accra.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments