Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu da ta bada belin Omoyele Sowore kan kuɗi Naira miliyan 200

Kotu da ta bada belin Omoyele Sowore kan kuɗi Naira miliyan 200

Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, sabon beli kan kuɗi Naira miliyan 200 a shari’ar da ake tuhumarsa da laifukan da suka shafi dokar laifukan intanet (Cybercrime).

Mai shari’a Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne a ranar Talata, bayan kotun ta soke belin da aka ba Sowore a baya sakamakon rashin halartarsa a zaman kotu.

A cewar kotun, Sowore zai cika waɗannan sharuɗɗa kafin ya fita beli:

Ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Ɗaya daga cikin masu tsayawa masa dole ne ya kasance basarake daga garinsu da ke ƙaramar hukumar Ese-Odo ta jihar Ondo.

Na biyun kuma dole ne ya mallaki fili ko gida a Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Masu tsaya masa za su fuskanci tantancewa daga masu gabatar da ƙara.

Haka kuma, kotun ta umarce shi da ya miƙa fasfo ɗinsa na ƙasa da ƙasa ga Mataimakin Babban Magatakardar Kotu har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments