Ƙasar Qatar ta yi Allah-wadai da kutsen da sojojin Isra’ila suka yi cikin ƙasar Siriya, tana mai bayyana hakan a matsayin babban take haƙƙin ikon ƙasar da kuma karya dokokin ƙasa da ƙasa.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta ce hare-haren sun haɗa da luguden wutar manyan bindigogi kan wasu yankuna a lardunan Quneitra da Deraa, lamarin da zai ƙara rura wutar rikici a yankin tare da kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya.
Qatar ta kuma buƙaci ƙasashen duniya da su matsa wa Isra’ila lamba domin ta mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.
A ranar Lahadi, sojojin Isra’ila sun kai hari kan ƙauyen Abdeen da ke yammacin lardin Deraa ta amfani da manyan bindigogi da jiragen yaƙin sama masu saukar ungulu, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa daga gidajensu.