Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nazarin hanyoyin da za su inganta jin daɗi da walwalar ma’aikatan ɓangaren yaɗa labarai a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin bikin Makon Ma’aikatan Gwamnati na shekarar 2026 da aka gudanar a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.
A cewarsa, gwamnati na da niyyar ƙarfafa gwiwar ma’aikatan ɓangaren ta hanyar samar da ingantattun tsare-tsaren walwala domin ƙara ƙwazon aiki da kuma habbaka ayyukan yaɗa labarai.
A wajen bikin, an kuma karrama wasu ma’aikata da takardun yabo saboda ƙwarewa, jajircewa da gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ma’aikatar.