Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro’Yan bindiga sun kashe mutum 18, sun jikkata sama da 20 a...

’Yan bindiga sun kashe mutum 18, sun jikkata sama da 20 a sabon hari a Plateau

Mahara Sun Kai Farmaki Bokkos, Sun Kashe Mutane 18 3. Jini Ya Sake Zuba a Plateau Bayan Harin Mahara Kan Garuruwa Biyu

Akalla mutane 18 sun rasa rayukansu yayin da wasu mahara masu ɗauke da makamai suka kai mummunan hari garuruwan Kawel da Kopkon da ke Gundumar Mushere a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Plateau a daren Lahadi.

Shugaban matasan Bokkos, Christopher Luka, ya bayyana cewa maharan sun kutsa cikin al’ummomin yankin tare da buɗe wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 18, yayin da fiye da mutum 20 suka samu raunuka daban-daban.

Majiyoyin tsaro sun ce dakarun Operation Enduring Peace sun garzaya wuraren bayan samun rahoton harin, inda suka gano gawarwaki 12 a ƙauyen Kawel, sai kuma wasu shida a Kopkon.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tsere daga wurin kafin isowar jami’an tsaro.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike da sintiri a yankunan da abin ya shafa domin gano tare da cafke waɗanda suka kai harin.

Wannan sabon hari na zuwa ne bayan kwanaki kaɗan da kashe Hakimin Gwande, Samuel Alaket, a wani kwanton bauna a Bokkos.

Hare-haren da ake ci gaba da fuskanta a wasu sassan Plateau cikin watan Yuni sun ƙara nuna irin ƙalubalen tsaron da jihar ke fama da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments