Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMazraoui ka iya jingine takalmin sa domin cimma burinsa na haddace Alkur’ani...

Mazraoui ka iya jingine takalmin sa domin cimma burinsa na haddace Alkur’ani mai girma

Ɗan wasan ƙasar Morocco, Noussair Mazraoui, ya bayyana cewa yana iya yiwuwa ya yanke shawarar yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa bayan kammala gasar cin Kofin Duniya.

Ɗan wasan ƙasar Morocco, Noussair Mazraoui, ya bayyana cewa yana iya yiwuwa ya yanke shawarar yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa bayan kammala gasar cin Kofin Duniya.

Mazraoui ya ce rayuwa gajera ce, don haka yana tunanin yadda zai mayar da hankali ga abubuwan da suka fi masa muhimmanci a rayuwa bayan wasanni.

Ya ƙara da cewa yana da burin zurfafa ilimin addini, musamman ta hanyar haddace Al-Qur’ani mai girma, tare da fata cewa wata rana zai zama Limamin masallaci.

Kalaman nasa sun ja hankali sosai a kafafen sada zumunta, inda magoya baya ke bayyana ra’ayoyi daban-daban kan yiwuwar wannan mataki, musamman ganin cewa yana daga cikin fitattun ‘yan wasan da ke taka rawar gani a matakin ƙasa da ƙasa.

Har yanzu dai ba a tabbatar da cikakken matakin da zai ɗauka ba, amma kalamansa sun nuna cewa yana tunanin makomarsa bayan harkar ƙwallon ƙafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments