Sunday, October 18, 2026
HomeTsaro’Yan bindiga sun ƙone sansanin NSCDC a Kebbi

’Yan bindiga sun ƙone sansanin NSCDC a Kebbi

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari sansanin jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) da ke ƙauyen Tsamiya, a ƙaramar hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka ƙone sansanin tare da yin garkuwa da wani mazaunin yankin.

Rahotanni sun ce maharan sun mamaye garin ne cikin daren Asabar, suka riƙa harbe-harbe tare da banka wa wasu gine-gine wuta, ciki har da sansanin NSCDC da gidan wani mazaunin yankin. Sun kuma sace wani mutum mai suna Alhaji Yusuf Bazamfare.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da harin, inda ta bayyana cewa tuni Kwamishinan ‘Yan Sanda ya umarci tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya. Haka kuma, an fara bincike tare da ci gaba da ƙoƙarin ceto wanda aka sace da kuma kamo waɗanda suka kai harin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments