Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yaba wa al’ummar Jihar Ekiti saboda gudanar da zaɓen cikin lumana da nuna amincewarsu ta hanyar sake zaɓen Oyebanji domin ci gaba da jagorantar jihar.
Shugaban ya ce sakamakon zaɓen ya nuna yadda al’ummar jihar ke gamsuwa da irin shugabanci da gwamnatin Oyebanji ta bayar, tare da yi masa fatan ci gaba da gudanar da mulki cikin adalci da ci gaba.