Amurka da Iran sun fara wata sabuwar tattaunawa a ƙasar Switzerland domin rage zaman ɗarɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu, musamman kan shirin nukiliyar Iran.
A zaman farko na tattaunawar, Amurka ta buƙaci Iran ta bai wa masu binciken Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya (IAEA) damar shiga tare da duba cibiyoyin nukiliyarta da ake takaddama a kansu.
Rahotanni sun ce a madadin hakan, Amurka ta yi tayin bai wa Iran damar samun wani ɓangare na kuɗaɗenta da aka daskarar a ƙasashen waje, ciki har da dala biliyan 6 da ke ajiye a ƙasar Qatar.
Majiyoyi sun bayyana cewa Amurka na fatan Iran za ta amince da wannan buƙata a matsayin matakin farko na gina amincewa tsakanin ɓangarorin biyu da kuma ci gaba da tattaunawar.
Sai dai har yanzu Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan ko za ta amince da tayin da Amurka ta gabatar ba.