Hezbollah ta sanar da cewa ta kashe tare da raunata wasu sojojin Isra’ila a wani hari da ta kai a Kudancin Lebanon.
Ƙungiyar ta ce mayaƙanta sun lalata tankokin yaƙi uku kirar Merkava bayan sun kai musu kwanton bauna, kafin su ci gaba da luguden wuta kan dakarun Isra’ila.
Sai dai sojojin Isra’ila sun tabbatar da mutuwar sojoji huɗu, ciki har da kwamandan rundunar tankokin yaƙi, yayin da suka ce harin ya afku ne lokacin da suke gudanar da aiki a Kudancin Lebanon.
A lokaci guda kuma, hare-haren saman Isra’ila kan yankunan Kudancin Lebanon sun yi sanadin mutuwar mutane 24 tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ke nuna ci gaba da tsananta rikicin.