Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLikitoci dubu 55 ne kacal suka rage domin kula da ’yan Najeriya...

Likitoci dubu 55 ne kacal suka rage domin kula da ’yan Najeriya miliyan 220

Likitoci sun yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar matsanancin ƙarancin ma’aikatan lafiya, inda likitoci kusan 55,000 kacal suka rage suna kula da al’ummar da yawansu ya haura miliyan 220.

Likitoci sun yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar matsanancin ƙarancin ma’aikatan lafiya, inda likitoci kusan 55,000 kacal suka rage suna kula da al’ummar da yawansu ya haura miliyan 220.

An bayyana hakan ne a taron Ƙungiyar Likitocin ma su neman Kwarewa ARD na Asibitin Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa da ke Yaba, Legas, inda suka ce yawaitar kaura na likitoci na ƙara raunana harkar lafiya, musamman fannin kula da masu matsalar ƙwaƙwalwa.

A cewarsu, sama da likitoci 16,000 sun bar Najeriya cikin shekaru biyar da suka gabata domin neman aiki a ƙasashen waje, lamarin da ya ƙara nauyi kan waɗanda suka rage tare da rage damar jama’a wajen samun ingantacciyar kulawar lafiya.

Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya NMA, Farfesa Omoti Ernest, ya ce duk da cewa an yi wa likitoci sama da 130,000 rajista a ƙasar, kusan 55,000 ne kawai ke aiki a halin yanzu. Ya yi kira ga gwamnati da ta inganta albashi, yanayin aiki da kayan aikin asibitoci domin dakile ci gaba da ficewar likitoci zuwa ƙasashen waje.

SourceVanguard
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments