Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwankwaso ya mara wa sabuwar dokar NDC baya

Kwankwaso ya mara wa sabuwar dokar NDC baya

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana goyon bayansa ga sabuwar dokar da jam’iyyar ta bullo da ita domin dakile sauya sheƙar ’yan siyasa bayan sun ci zaɓe.

Sabuwar dokar ta tanadi cewa duk wani ɗan takarar da zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar zai sanya hannu kan takardar alƙawarin cewa zai ajiye kujerarsa idan ya sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya bayan cin zaɓe.

Jam’iyyar ta ce wannan zai zama sharadi kafin a miƙa sunayen ’yan takara ga INEC.

A cewar jam’iyyar, manufar matakin ita ce kare ƙuri’un al’umma, ƙarfafa da’a da biyayya ga jam’iyya tare da rage yawaitar sauya sheƙa bayan an samu nasara a zaɓe.

Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mohammed, ya ce wannan tsari ya yi daidai da abin da ƙungiyar ta daɗe tana kira a kai na mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma bin dokokin jam’iyya.

Ya ƙara da cewa Kwankwasiyya ta taɓa fuskantar irin wannan ƙalubale a baya bayan wasu manyan jiga-jiganta sun sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyu, lamarin da ya ce ya jawo cikas ga tafiyar ƙungiyar.

Sai dai jam’iyyar ta bayyana cewa wannan sabon sharadi ba zai shafi ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments