Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta sanar da karɓar ƴan Najeriya 180 da aka dawo da su daga ƙasar Algeria, a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.
NEMA ta bayyana cewa an dawo da mutanen ne ƙarƙashin shirin maido da ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje bisa radin kansu, wanda ake aiwatarwa tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ƙaurar Baƙi ta Duniya (IOM) da sauran hukumomin gwamnati.
Waɗanda aka dawo da su sun haɗa da maza 134, mata 38, yara maza huɗu, yara mata biyu, da jarirai biyu – mace ɗaya da namiji ɗaya. Sun isa Legas ne a ranar Talata, 16 ga Yunin 2026.
Bayan isowarsu, jami’an Hukumar Shige da Fice ta Najeriya sun yi musu rajista tare da tattara bayanansu ta hanyar na’ura domin sauƙaƙa shirin mayar da su jihohin da suka fito.
Hukumar NEMA ta ce ta kuma samar musu da tallafin gaggawa da ya haɗa da abinci, ruwan sha, kula da lafiya da kuma ɗaukar nauyin jigilar su zuwa garuruwansu domin sauƙaƙa komawarsu cikin al’umma.