Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da asusun tallafi na Naira miliyan 50 domin taimaka wa masu fama da cutar daji, musamman waɗanda ke fuskantar matsalolin kuɗi da ke hana su samun cikakkiyar kulawar lafiya.
Karamin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Dakta Iziaq Salako, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin kaddamar da rabon tallafin ga marasa lafiya.
Ya ce an kafa asusun ne domin rage wa marasa lafiya nauyin da ba na magani ba kamar kuɗin sufuri, masauki, abinci da kuma rashin tallafin iyali, waɗanda galibi ke hana su ci gaba da jinya.
A cewarsa, sama da mutane 600 sun nemi tallafi, inda aka amince da fiye da 200 bayan cikakken tantancewa daga likitoci da masu kula da su.
Ministan ya ƙara da cewa duk wanda aka tabbatar ya cancanta zai samu aƙalla Naira 100,000 domin taimaka masa wajen tafiyar da jinya.