Akwai yiwuwar a samu ƙarin kuɗin kira da tura saƙonnin kar ta kwana, SMS tsakanin hanyoyin sadarwa, yayin da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ke nazarin kuɗin haɗa kira tsakanin kamfanonin sadarwa, wani tsari da ba a sake dubawa ba tun shekarar 2018.
Hukumar ta ce sauye-sauyen tattalin arziki da ƙarin kuɗin gudanar da ayyuka ne suka sa ake yin wannan nazari. Masana na ganin sakamakon hakan na iya shafar farashin kira da SMS da masu amfani ke biya.
Sai dai NCC ta bayyana cewa har yanzu ba a yanke hukuncin ƙara kuɗin kira ko SMS ba, domin nazarin na ci gaba.