Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiKotun Ɗaukaka Ƙara Ta Dakatar Da Hukuncin Soke Rajistar ADC Da Wasu...

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Dakatar Da Hukuncin Soke Rajistar ADC Da Wasu Jam’iyyu

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta ba da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta ba da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.

Kotun ta umarci INEC da kada ta ci gaba da soke rajistar jam’iyyun har sai an kammala sauraron ƙarar da jam’iyyun suka shigar.

A ranar Litinin, Alƙali Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya ya umarci soke rajistar ADC, da Accord Party da wasu jam’iyyu bisa zargin gaza cika wasu sharuɗɗan kundin tsarin mulki.

Sai dai kwamitin alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya soki hukuncin kotun ƙasa, yana mai bayyana matakin a matsayin abin da ya saɓa da tsarin shari’a da mutunta manyan kotuna.

Saboda haka, rajistar jam’iyyun na ci gaba da aiki har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe kan shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments