Manoma da makiyaya daga yankuna daban-daban na jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da ake fatan za ta kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka daɗe suna faruwa a tsakaninsu.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 9 ga Yunin 2026 a yankin Sarkin Yamma, inda wakilan bangarorin biyu daga gundumomin Safo, Sarkin Yamma, Tibiri da kuma birnin Maradi suka halarci taron.
Gwamnan yankin Maradi, Kontrolan ’Yan Sanda Issoufou Mamane, ne ya jagoranci taron, tare da halartar Sarkin Katsina-Maradi, Ahmed Ali Zaki, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati, shugabannin al’umma da kuma jami’an tsaro.
Yarjejeniyar ta biyo bayan shafe watanni takwas ana gudanar da tattaunawa da zaman sulhu ƙarƙashin jagorancin Cibiyar Jinƙai ta Shiga Tsakani (HD), bisa haɗin gwiwar hukumomin yankin da shugabannin gargajiya.
A yayin zaman sulhun, an tattauna hanyoyin warware sabanin da ke tasowa tsakanin manoma da makiyaya kan amfani da filaye, hanyoyin kiwo, ruwa da sauran albarkatun da ke cikin kwarin Goulbi Maradi.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da kuma bunƙasa ayyukan noma da kiwo cikin lumana a yankin.