Monday, October 19, 2026
HomeTsaroKwankwaso ya nemi a gaggauta ceto dalibai da malamai da aka sace...

Kwankwaso ya nemi a gaggauta ceto dalibai da malamai da aka sace a Oyo

Tsohon gwamnan Kano ya nuna damuwa kan sace dalibai a jihar Oyo

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana matukar damuwarsa kan sace dalibai da malamai daga wasu makarantu a karamar hukumar Oriire da ke Jihar Oyo.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su dauki lamarin a matsayin abin gaggawa tare da kara kaimi wajen ceto dukkan wadanda aka sace cikin koshin lafiya.

Ya ce abin takaici ne yadda har yanzu makarantu da cibiyoyin ilimi ke ci gaba da fuskantar hare-haren masu garkuwa da mutane, yana mai jaddada cewa dole ne gwamnati ta dauki tsauraran matakan da za su hana sake aukuwar irin wadannan hare-hare a nan gaba.

Kwankwaso ya kuma yi kira da a karfafa tsaro a makarantu, musamman wadanda ke yankunan karkara, domin kare rayukan dalibai da malamai da kuma tabbatar da cewa ilimi ba ya fuskantar barazana daga matsalolin tsaro.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments