Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciRikicin Hormuz na barazana ga kasuwancin Afrika – Dangote

Rikicin Hormuz na barazana ga kasuwancin Afrika – Dangote

Dangote ya yi gargadi kan matsin da ƴan kasuwar Afrika ke fuskanta

Attajirin nahiyar Afrika, Aliko Dangote ya bayyana damuwarsa kan irin matsin tattalin arziki da matsalolin kasuwanci da ƴan kasuwar Afrika ke fuskanta sakamakon tangardar da ake samu a harkokin sufuri da kasuwancin duniya.

Dangote ya yi wannan bayani ne yayin ziyarar duba aikin wata babbar masana’antar taki da ake shirin ginawa a kudu maso gabashin Habasha, wadda ake sa ran za ta samar da tan miliyan uku na taki duk shekara.

Ya ce rikice-rikicen da suka shafi mashigin Hormuz na kawo tsaiko wajen safarar kayayyaki da shigo da haja zuwa Afrika, lamarin da ya haddasa tashin farashin kayayyaki musamman taki a kasuwannin duniya.

A cewarsa, kaso mai yawa na takin duniya na bi ta mashigin Hormuz, don haka duk wata matsala da ta shafi yankin na iya yin tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin Afrika da harkokin kasuwanci.

@⁨

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments