Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAPC: Ana zargin shirin hana ATM Gwarzo takarar Sanatan Kano ta Arewa

APC: Ana zargin shirin hana ATM Gwarzo takarar Sanatan Kano ta Arewa

Ana zargin hannun Sanata Barau wajen ƙoƙarin hana ATM Gwazo neman takarar Sanatan Kano ta Arewa

Wani sabon rikici ya ɓarke a cikin jam’iyyar APC bayan zargin cewa wasu manyan mutane a jam’iyyar na ƙoƙarin hana tsohon minista, Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano ta Arewa.

Rahoton ya ce ana zargin wasu masu ruwa da tsaki a APC na son hana ATM Gwarzo shiga zaɓen fidda gwani domin bai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, damar samun tikitin jam’iyyar ba tare da wata hamayya ba.

Wata majiya daga hedkwatar APC ta ƙasa, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa akwai yiwuwar a hana ATM Gwarzo tsallake tantancewar ’yan takara kafin zaɓen fidda gwani da aka shirya yi ranar 18 ga Mayu, 2026.

Majiyar ta ce ana matsa lamba sosai kan kwamitin tantancewar domin a cire sunan ATM Gwarzo daga masu neman takarar.

Ta ƙara da cewa ko da ya tsallake matakin tantancewa, akwai fargabar cewa za a iya cire sunansa daga jerin sunayen waɗanda aka amince da su kafin ranar zaɓe.Rahoton ya ce wannan lamari ya ƙara tayar da hankali tsakanin jiga-jigan APC a Kano, inda mutane da dama ke sa ido kan yadda abubuwa za su kaya kafin zaɓen fidda gwanin.

A wani ɓangaren kuma, wasu majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawar sirri da wasu manyan ’yan siyasa a Kano, ciki har da tsofaffin gwamnoni Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

An ce a wajen taron, ATM Gwarzo ya zargi Sanata Barau Jibrin kai tsaye da hannu wajen hana shi tsallake tantancewa a zaɓen da ya gabata lokacin gwamnatin Ganduje.

Rahoton ya ce idan aka sake hana ATM Gwarzo takara a wannan karo, zai zama karo na biyu da ake zargin Sanata Barau yana da hannu wajen hana shi samun damar shiga zaɓen fidda gwani na Sanatan Kano ta Arewa.

Duk da matsin lambar da ake zargin ana yi masa, an ce ATM Gwarzo ya sha alwashin ba zai janye daga takarar ba, yana mai kira ga APC ta gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani da adalci kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.Sanata Barau Jibrin bai ce komai game da zarge-zargen ba.

Haka kuma, mai ba Sanata Barau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Isma’il Mudassir, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Ana sa ran APC za ta gudanar da zaɓen fidda gwani na sanatoci a faɗin ƙasar nan ranar 18 ga Mayu, 2026, yayin da takarar Kano ta Arewa ke ci gaba da ɗaukar hankalin mutane da dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments