Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFursunoni 9 a Kano sun haddace Alƙur’ani mai girma a gidan gyaran...

Fursunoni 9 a Kano sun haddace Alƙur’ani mai girma a gidan gyaran hali

Mutane tara daga cikin fursunonin da ke zaman hukunci a gidan gyaran hali na matsakaicin tsaro da ke Wudil a Jihar Kano sun samu nasarar kammala haddar Alƙur’ani mai tsarki gaba ɗaya.

Mutane tara daga cikin fursunonin da ke zaman hukunci a gidan gyaran hali na matsakaicin tsaro da ke Wudil a Jihar Kano sun samu nasarar kammala haddar Alƙur’ani mai tsarki gaba ɗaya.

Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin bikin cika shekaru 50 da kafuwar cibiyar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar gidajen gyaran hali ta Najeriya a Jihar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan fursunoni ba su da cikakken ilimin karatun Alƙur’ani kafin shigarsu cibiyar, amma ta hanyar jajircewa, ladabi da kuma koyarwa mai tsari, sun samu nasarar haddace shi gaba ɗaya.

Ya ce wannan nasara na nuna yadda hukumar ke ƙoƙarin gyara halaye, horaswa da kuma mayar da fursunoni cikin al’umma yadda ya dace, bisa tanadin dokar gyaran hali ta shekarar 2019.

Ya kuma ƙara da cewa tsawon lokaci, cibiyar Wudil ta zama abin koyi wajen samar da ilimi, koyon sana’o’i da kuma shirye-shiryen tarbiyya ga fursunoni.

Haka kuma, ya ce shugaban rundunar a jihar, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yaba wa babban shugaban gidajen gyaran hali na ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa ƙoƙarinsa na inganta shirye-shiryen ilimi da koyon sana’o’i a dukkan gidajen gyaran hali na ƙasar.

A cewarsa, irin waɗannan shirye-shirye suna da muhimmanci wajen bai wa fursunoni damar dogaro da kai da kuma komawa cikin al’umma cikin nasara bayan sun kammala hukuncinsu.

Shugaban cibiyar ta Wudil, Ibrahim Wada Ibrahim, ya gode wa rundunar jihar bisa goyon baya, yana mai cewa wannan nasara alama ce ta shugabanci nagari da kuma himma wajen inganta rayuwar fursunoni.

Shi ma shugaban jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya yaba da wannan ƙoƙari, yana mai cewa irin wannan shiri yana taimakawa sosai wajen sauya rayuwar fursunoni domin su zama ‘yan ƙasa nagari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments