Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan bindiga sun harbe wani fasto gami da sace wasu masu ibada...

Yan bindiga sun harbe wani fasto gami da sace wasu masu ibada a jihar Ekiti

Fargaba da tashin hankali sun barke a ƙauyen Eda Oniyo da ke ƙaramar hukumar Ilejemeje a Jihar Ekiti a daren Talata, bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wani coci yayin wani taron wa’azi na fili.

Fargaba da tashin hankali sun barke a ƙauyen Eda Oniyo da ke ƙaramar hukumar Ilejemeje a Jihar Ekiti a daren Talata, bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wani coci yayin wani taron wa’azi na fili.

Rahotanni sun nuna cewa maharan, dauke da manyan makamai, sun kai farmaki wurin taron da ke wajen gari da yawa, inda suka bude wuta, suka kashe wani Fasto tare da sace masu ibada da dama.

Majiyoyi daga cikin al’ummar yankin sun bayyana cewa maharan sun shafe wasu mintuna suna aikata ta’asar kafin su tafi da wadanda suka sace zuwa cikin daji.

Wani mazaunin yankin ya ce: “Da yammacin yau ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari wani coci a wajen gari a Eda Oniyo yayin wani shirin ibada. Sun sace mutane da dama ciki har da tsofaffi da yara.”

Ya kara da cewa: “Sun harbe Faston sannan suka tafi da masu ibada zuwa cikin daji. Maharan sun zo da yawa kuma suna dauke da makamai.”

Ko da yake ba a tantance adadin mutanen da abin ya shafa ba a yanzu, lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin firgici.

Wani babban jami’in gwamnati kuma memba na kwamitin tsaro na jihar, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an riga an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin bin diddigin maharan.

Ya bayyana cewa: “Eh, an sace wasu masu ibada a Eda Oniyo a yau, amma jami’an tsaro suna aiki tukuru. Gwamnati ta tura jami’ai kuma suna bin sawun maharan domin ceto wadanda aka sace cikin koshin lafiya.”

Ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa za a kubutar da wadanda aka sace ba tare da lahani ba, yana mai jaddada cewa hukumomi ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen magance matsalar.

A kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda, an kasa samun amsa daga jami’in hulda da jama’a na rundunar, domin ba a amsa kiran waya da sakonnin da aka aika masa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments