Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFitar da man jiragen sama daga matatar Dangote ya ƙaru da kashi...

Fitar da man jiragen sama daga matatar Dangote ya ƙaru da kashi 770 cikin shekaru biyu

Adadin man jiragen sama da matatar mai ta Dangote ke fitarwa ya ƙaru da kusan kashi 770 cikin ɗari a cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon ƙaruwa buƙatar wannan man a kasuwannin duniya da kuma faɗaɗa ƙarfin matatar.

Adadin man jiragen sama da matatar mai ta Dangote ke fitarwa ya ƙaru da kusan kashi 770 cikin ɗari a cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon ƙaruwa buƙatar wannan man a kasuwannin duniya da kuma faɗaɗa ƙarfin matatar.

Bincike daga bayanan jigilar kayayyaki na kamfanin Kpler ya nuna cewa matatar Dangote ta sauya daga wata sabuwar matata a yankin zuwa zama babbar mai samar da man jiragen sama a duniya cikin ɗan lokaci kaɗan.

A watan Afrilu na 2026, fitar da man ya kai kusan ganga 158,000 a rana, idan aka kwatanta da ganga kusan 18,000 a rana a Afrilu 2024 lokacin da aka fara fitarwa.

A farkon fara aiki a 2024, ba a kai man zuwa Turai ba, amma zuwa Afrilu 2026, an kai kusan ganga 70,000 a rana zuwa Turai. Haka kuma, fitar da man zuwa ƙasashen Afirka ya ƙaru daga ganga 18,000 zuwa 69,000 a rana, wanda ya nuna ƙaruwa mai yawa.

Wannan ci gaban ya samu ne saboda rikicin Gabas ta Tsakiya wanda ya sa kasashen Turai ke neman sabbin hanyoyin samun man jiragen sama, inda matatar Dangote ke zama madadin da ya fi kusa da aminci.

Haka kuma, matatar ta taimaka wajen rage dogaro da shigo da man jiragen sama daga Turai da Asiya zuwa kasashen Afirka, tare da samar da man a yankin cikin sauƙi.

Bayan Turai da Afirka, kasashen Amurka ma sun kasance kasuwa mai muhimmanci, kodayake fitar da man zuwa can yana canzawa lokaci zuwa lokaci.

Bayanan sun kuma nuna cewa daga Disamba 2025 zuwa Afrilu 2026, jimillar fitar da man ta tashi daga ganga 81,000 zuwa 158,000 a rana, ƙaru da kashi 95 cikin ɗari cikin watanni huɗu kacal.

Wannan ya nuna yadda matatar Dangote ke da ƙarfin daidaitawa da sauri domin biyan bukatun kasuwar duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments