Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaSanata Natasha na shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin tarar Naira biliyan ɗaya

Sanata Natasha na shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin tarar Naira biliyan ɗaya

Sanata Natasha za ta kalubalanci hukuncin tarar naira biliyan ɗaya a kotu.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta umurci lauyoyinta da su ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotu da ya ba tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, diyyar Naira biliyan 1 kan zargin ɓata suna.

Ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi ga magoya bayanta a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook jim kaɗan bayan yanke hukuncin.

Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ce ba za ta amince da hukuncin ba, tana mai cewa kotun ba ta yi la’akari da hujjojin da ɓangaren ta ya gabatar ba yadda ya kamata.

Ta kuma jaddada cewa za ta kai ƙarar har zuwa Kotun Ƙoli idan ya zama dole.

A yayin jawabin, ta sake yin tsokaci kan zarge-zargen da gwamnatin jihar Kogi ta yi mata a 2022 na alaƙa da ayyukan ta’addanci, ciki har da harin gidan yari na Kuje da na cocin Owo, tana mai cewa tana waje a lokacin da abubuwan suka faru kuma ba ta da hannu a ciki.

Ta kuma zargi Yahaya Bello da ƙoƙarin sa a kama ta domin hana ta shiga zaɓe, tana mai cewa zarge-zargen na siyasa ne.

Haka kuma ta bayyana damuwa kan matsalar tsaro a jihar Kogi, inda ta ce ana fama da tsoro, tashin hankali da kuma ɓacewar mutane a wasu yankuna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments