Ƴan Majalisar dokokin Amurka sun bukaci ma’aikatar tsaro ta ƙasar ta Pentagon ta yi cikakken bayani kan hare-haren sama da Amurka ta kai a Najeriya a ranar 25 ga Disamba, 2025, tare da bayyana irin matsayin sojojin Amurka a kasar gaba ɗaya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar cewa sojojin ƙasar sun kai hare-hare kan mayaƙan da ake dangantawa da kungiyar IS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa daga baya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an gudanar da wannan aiki a jihar Sakkwato da izininta, kuma bai karya ikon Najeriya ko iyakokinta ba.
Sai dai a wata wasika da aka rubuta ranar 9 ga Maris, 2026 zuwa ga shugaban tsaron Amurka, Pete Hegseth, ‘yan majalisar karkashin jagorancin Sara Jacobs da Jason Crow sun bukaci karin haske kan yadda aka gudanar da aikin.
Wasikar, wacce aka kuma aika wa shugaban rundunar sojojin Amurka a Afirka, Dagvin Anderson, da mikistan harkokin Waje, Marco Rubio, ta nemi bayanai kan batun doka, hadin gwiwa da hukumomin Najeriya, da kuma rahotannin da ke nuna yiwuwar asarar rayukan fararen hula.
‘Yan majalisar sun ambaci cewa gwamnatin Amurka ta bayyana hare-haren a matsayin nasara ba tare da an samu kuskure ba, amma sun ce babu sahihin hujja a bainar jama’a da ke nuna akwai ISIS a jihar Sakkwato.