Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGaro ya godewa gwamna Abba tare da jaddada ƙudurin sa na kawo...

Garo ya godewa gwamna Abba tare da jaddada ƙudurin sa na kawo cigaba a Kano

Murtala Sule Garo, ya mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da ya yi na mika sunansa ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin mataimakin gwamna.

Garo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba.

“Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya raya mu ya kuma kai mu wannan lokaci cikin koshin lafiya da wannan bigire na rayuwa da siyasa.”

Ya kara da cewa nadin da aka yi masa ba kawai karramawa ba ce, illa babban nauyi ne na hidimtawa al’ummar jihar Kano.

“Wannan mataki da Mai girma Gwamna ya dauka ba wai karramawa ce a gare ni kadai ba, babban kira ne zuwa ga sauke nauyi mai girma da hidima ga al’ummar Jihar Kano.”

Ya kuma gode wa shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da daukacin al’ummar Kano bisa goyon baya da addu’o’in da suke ba shi.

“Ina mika godiya ta musamman ga shugabannin jam’iyyarmu da daukacin al’ummar Kano bisa kauna, addu’o’i da goyon baya. Wannan goyon baya na da matukar muhimmanci wajen kara mana azama.”

Garo ya yi kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyya, ciki har da wadanda suka nemi mukamin, da su hada kai domin cigaban jihar.

“Ina kira ga dukkan shugabanni da mambobin jam’iyya da mu kara hada kai cikin kauna da ‘yan uwantaka domin cigaban Jihar Kano.”

Ya kuma tabbatar da kudurinsa na aiki tukuru domin tallafawa manufofi da shirye-shiryen ci gaban da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa.

“Zan ci gaba da sadaukar da kai da biyayya tare da aiki tukuru domin karfafa hadin kai da kuma tallafawa manufofin ci gaba da Mai girma Gwamna ya assasa.”

Ya ce da yardar Allah zai bayar da gudunmawa wajen ganin gwamnatin Kano ta cimma nasarori masu dorewa a fannoni daban-daban.

SourceCNN
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments