Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTsofaffin ƴan sanda sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa aka tsarin fansho...

Tsofaffin ƴan sanda sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa aka tsarin fansho da suke kai

Tsofaffin jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin, inda suka toshe wata ƙofa ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, suna nuna rashin jin daɗinsu kan ci gaba da saka su cikin tsarin fansho na CPS.

Masu zanga-zangar, karkashin ƙungiyar Police Retired Officers Forum of Nigeria, PROF, sun bayyana tsarin a matsayin na yaudara, rashin adalci da kuma rashin tausayi, suna kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya rattaba hannu kan dokar fitar da ‘yan sanda daga wannan tsari.

A cewarsu, dokar da Majalisar Tarayya ta amince da ita a ranar 4 ga Disamba, 2025, kuma aka miƙa wa fadar shugaban ƙasa a ranar 16 ga Maris, 2026, idan aka sanya hannu a kanta, za ta cire jami’an ‘yan sanda daga tsarin CPS.

Jagoran zanga-zangar kuma mai kula da ƙungiyar na ƙasa, CSP Raphael Irowainu mai ritaya, ya ce manufar zanga-zangar ita ce matsa lamba ga shugaban ƙasa ya sanya hannu kan dokar domin ta zama doka.

Ya koka da cewa sauran hukumomin tsaro kamar sojoji, SSS, rundunar sojin sama da ta ruwa, da kuma hukumar leƙen asiri ta ƙasa duk an cire su daga tsarin, amma ‘yan sanda har yanzu suna ciki.

Masu ritayar sun ce tsarin CPS ya yi tasiri mara kyau ga rayuwarsu, suna ma bayyana shi a matsayin tsarin da ke jefa su cikin wahala da kuma gaggauta mutuwa garesu.

Wannan ba shi ne karo na farko da suke yin irin wannan zanga-zanga ba, domin a watan Yuli na 2025 ma sun yi irin wannan a Majalisar Tarayya, suna neman a cire su daga tsarin.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar, da dama daga cikinsu tsofaffi ne, sun kuma yi zanga-zanga a hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Abuja, suna kuka kan yadda tsarin fansho ke tafiya a halin yanzu.

Wannan sabuwar zanga-zangar ta nuna yadda rashin jin daɗi ke ƙaruwa a tsakanin tsofaffin jami’an ‘yan sanda kan batun gyaran tsarin fansho da kuma rashin samun wasu fa’idoji da sauran hukumomin tsaro ke morewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments