Hukumar kula da harkokin yaɗa labarai ta Najeriya, NBC, ta gargadi gidajen rediyo da talabijin kan cin zarafin baƙi a shirye-shiryensu, amfani da dandamali ba daidai ba, da kuma karya dokokin yaɗa labarai gabanin zaben 2027.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwa wajen karya dokokin yaɗa labarai na ƙasa bugu na 6, musamman a shirye-shiryen labarai da na siyasa. Ta ce wasu kafafen watsa labarai sun kauce daga aikinsu na wayar da kai cikin gaskiya da ƙwarewa, don haka za ta dauki mataki mai tsauri wajen tabbatar da bin dokoki.
NBC ta bayyana cewa yayin da ake shirin zaben 2027, za ta tabbatar da cikakken bin dokokin da suka shafi adalci, daidaito, sahihancin bayanai, gujewa kalaman ƙiyayya, kauce wa tunzura jama’a, da kuma girmama hukumomin ƙasa.
Haka kuma, hukumar ta nuna damuwa kan yadda wasu masu gabatar da shirye-shirye ke nuna rashin ƙwarewa, tana mai jaddada cewa dokar ta hana su bayyana ra’ayinsu. Ta kuma ce dole ne a bai wa kowane bangare damar bayyana ra’ayinsa domin tabbatar da adalci da daidaito.
NBC ta kara da cewa dole ne kafafen yaɗa labarai su guji kalaman ƙiyayya, tsokana ko rarrabuwar kai, musamman a shirye-shiryen siyasa. Ta kuma yi gargadi kan yadda ake mu’amala da baƙi, inda ta ce bai kamata a tsoratar da su ko nuna son kai ba.
Hukumar ta ce an lura da yadda ‘yan siyasa ke amfani da kafafen yada labarai ta hanyar da ba ta dace ba, wanda ya haifar da karuwar karya dokoki daga bangarori daban-daban.
NBC ta gargadi cewa duk wani mai gabatar da shiri da aka samu da bayyana ra’ayinsa, cin zarafin baƙo, ko hana wani bangare damar bayyana ra’ayinsa, za a dauki mataki a kansa.